KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐01/RABEE'UL-ULA/1440-HJRY
🌐09/NOVEMBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA= Abubakar BN Mustafa Biu

🔶 TOPIC➖[[KOWACE RAI ZATA DANDANI MUTUWA♨]]

🔹NA KASASHI GIDA 8⃣

1⃣➖MUQADDIMA‼
   Ba makawa kowa zai mutu❗babba ko karami! miji ko mace! fari ko baki! mawadaci ko talaka! musulmi ko kafiri,
SUBHANALLAH! dubi yadda MUTUWA ke mana bazata yana mana diban Karan mahaukaciya❗don haka dolene mutanada ayyuka nagari masu tseratarwa daga azaba😢

2⃣➖MUTUWA HAQIQA CE‼
   Yaku mutane! babu wani mutum dazai bar duniya face ya kutsa ta kunci da mayen MUTUWA kuma ya dandaneta❗
💡ALLAH SW yace <<kowace rai zata dandani MUTUWA>>[SRT ALI-IMRAN]

3⃣➖SALAF DA TSORONSA‼
💡ANNABI SAW yana neman tsari daga fitinar rayuwa da na mutuwa da azabar kabari da na wuta, kuma yana umurni da haka, harma a magagin mutuwarsa yana cewa "ya ALLAH katsareni daga mayen mutuwa Lalle mutuwa tanada maye"
▪ABI-HURAIRAH R/A- yayin mutuwarsa ance masa- meyasaka kuka⁉
Sai yace- nisan tafiya & karancin guzuri & raunin yaqini & tsoron fadowa daga kan siradi zuwa wuta

4⃣➖MAWAKI YAYIWA HALIFA WA'AZI‼
   Halifa HARUNAR RASHEED ya gina katafariyar bene, mawaka sun shigo sai yabawa suke, sai Mawaki ABUL-ATAHIYYA yashigo yayi yabo kamar haka=
 *karayu yadda kaso cikin inuwar kayataccen benennan cikin aminci # abubuwan da kake bukata suna kaikawo agareka safe da yamma.
   Halifa yayi farin ciki da wannan yabon, sai kuma ABUL-ATAHIYYA yakara cewa=
 *idan rayuka suka shiga gargara da nishinda aka tokarewa kirji # yayinne zaka sami yakinin abinda kakasance cikin rudune.
   Nan take HARUN yafashe da kuka yafadi kasa, yakulle benen yafasa kaurowa ciki yakoma tsohon gidansa,

5⃣➖YI TUNANI‼
📢Baiwar ALLAH! Bawan ALLAH!
Shin ka shiryawa MUTUWA⁉Shin afarke kake gareshi⁉Sau nawa labarin MUTUWAR matashi ke riskanka⁉ya mutu kwatsam❗ya gina gida🏘 kafin yashiga ya MUTU❗ya sayi mota🚐 kafin yahau ya MUTU❗yayita karatu kafin yakarbi takardar shaida ya MUTU❗ya tara miliyoyi kafin yaci ya MUTU❗dubi wancan da yatara dukkan nau'ika dukiyar duniya- in ya bar duniyane da wani abu koma bayan auduga da likkafani⁉

6⃣➖HOTON MUTUWAR FAJIRI‼
👂🏽 Wani mutum ne ya girma amma baisan ya girmaba, ya kama daki a otal yasa an kawo masa kwalaban giya🍾🍾🍾, yayita kwankwada, ashe matsiyacinnan baisan yana gab da ajalinsaba, yabugu kwarai da gaske saboda yasha dayawa, ya shiga ban daki bai fitoba sai bayan kwana 3 aka balla Kofar akaga gawarsa ya MUTU bakinsa akife da mazaunin bayan gidan garin amai,
SUBHANALLAH, abuge zai tashi agaban ALLAH a kiyama😭
 👂🏽Matasane su 4 suka tafi gidan rawa tsakar dare, sun sha giya suna rawa da karuwai💃🏻👯‍♂💃🏻, kwatsam sai daya cikin matasa hudun yafadi kasa yana shure shure, sai 'yan uwannasa ukun sukazo kansa sunata bashi kalmar shahada, shi kuma ya kasa furtawa, kusantowa me yake cewa⁉
Yana cewa= (Karo kofin giya🍷, wacce kuma kizo) wato yana neman karin giya kuma yana kiran karuwarsa, haka yake tacewa har ya MUTU,
SUBHANALLAH, haka zai tashi gaban ALLAH da ambaton giya da karuwa😭

7⃣➖HOTON MUTUWAR SALIHI‼
 👂🏽Wani mutum ne dattijo ya tsufa tsukuf, arayuwarsa shi mai sallar jam'ine akoda yaushe a masallaci🕌, yana cikin jinyar ajali sai yaji kiran sallar magrib, sai yacewa 'ya'yansa- kudaukeni zuwa masallaci,
Sai sukace masa- ya BABA, ai an maka uzurin zuwa jam'i tunda bakada lafiya, sai yace- ina jin kiran salla- bazanje masallaciba⁉kukaini masallaci nace,
   Suka kawoshi masallaci, a raka'a ta 3 ta karshe a sujadar karshe MUTUWA tadaukeshi,
ALLAHU AKBAR! Madalla da wannan MUTUWAR! zai tashi a gaban ALLAH da sujada😊

8⃣➖YIWA KANKA HISABI‼
   Bawan ALLAH! kayiwa kanka hisabi kafin MUTUWARKA❗
Me katanadar don gobe⁉
a wane hali Mala'ikan Mutuwa zai dauki ranka⁉
ya ya zaka hadu da mahaliccinka⁉
Shin ka tuba daga dukkan zunubbai⁉
Shin kana idda wajibai⁉
Shin kana maida amana ga masu ita⁉
Ko kuma ka gafalane samsam⁉

YA RABBANA KABAMU RAYUWA MAI KYAU A DUNIYA DA LAHIRA KUMA KATSAREMU DAGA AZABAR WUTAAAAA,😭😭😭
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via= Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽