KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐24/SAFAR/1440-HJRY
🌐02/NOVEMBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA= Abubakar BN Mustafa Biu

🔸TOPIC👉 [[CIRE ZAKKA]] & [[JINJINA & TA'AZIYYA GA 9jry ARMY]]
 ♨HADARIN YANKIN BIROM YAFI NA SAMBISA♨ domin SAMBISA ba mai zuwa‼

NA KASASHI GIDA 7⃣

1⃣➖MUQADDIMA‼
   Yaku Mutane! Kuji tsoron ALLAH kubada abinda ya wajibtar akanku daga dukiyoyinda ya azurtaku dashi ba da karfi ko dabararkuba, don ya fito daku daga cikkunan uwayenku bakusan komaiba sai yahuwace muku arziki gagara misali baku zataba, kugode masa kubada zakkar dukiyoyinku don ku tsarkakeshi, kuguji rowa domin yana lalata dukiya yacire albarkarsa,

2⃣➖KUGODEWA ALLAH‼
   Yaku Musulmai! Kugodewa ALLAH akan anfanin gonarda yabaku kukacisu danye kuka busarda wasu kuka dinkesu buhuhuna a ajiye, ALLAH ne yatsirar yagirmar yanunar yabusar ya nau'antata kala kala, Kugodewa ALLAH da yaja kwananku kuka riski girbinta yayinda wasu sun mutu kafin girbin nasu, kubada ZAKKARDA aka wajibtar muku acikinta don kuribatu da bunkasar dukiya a duniya da ladaddaki a lahira,

3⃣➖KUBADA ZAKKAR AMFANIN GONARKU‼
   Yaku Musulmai! Hakika muna cikin lokacin girbi da roro da tattara amfanin gona masara🌽 shinkafa da sauransu, kuma yanzune lokacin fitarda zakkarta, idan takai ausuki 5,
💡ANNABI SAW yace "in noman daminane acire 1 bisa 10, in noman ranine ½ bisa 10"

4⃣➖ZAKKA DA LA'AKKARI‼
   Akwai Malamai dasukace= in amfanin sunzo akwai masu kyau & tsaka tsaki & maras kyau to wajibine yacire ZAKKAR daga kowace nau'i gorgodonta,

5⃣➖KIRA GA KIN CIRE ZAKKA‼
   Yaku wadanda sukayi imani da ALLAH da ANNABINSA SAW❗Yaku wadanda suka gaskanta Qur'ani da Sunnah❗meye kimar dukiyarku da kuke rowar zakkarta⁉ Meye ribarku in kun mutu tazama mallakar wasu ku kuma an jefaku cikin Jahannama‼don haka kuji tsoron ALLAH kubada ZAKKAR da jin dadi aranku,
   Yaku masu kin bada ZAKKA! Kuna tsammanin in kun cire bazata amfaneku ba ko❓kuna tsammanin in kun cire kun bayar bazata amfaneku ba ko❓kuna ganinta asara ko❓
Na rantse da ALLAH mahaliccin tsirrai da busa rai- abinda kuka cire na ZAKKAR kuka bayar shine hakikanin ajiyarku da ribarku,
💡ALLAH SW yace <<abinda kuka gabatar don kanku zaku sameshi awurin ALLAH yafi alhairi da girman lada>>
   Wannan dukiyarda kuke rowarta ko kuci yakare ko ku mutu kubarwa wasu,
💡IYALAN ANNABI SAW sun yanka dabba sukayi sadaka da ita, sai ANNABI SAW yace musu "me yarage a naman?" sukace= ba abinda yarage sai kafadarta, sai ANNABI SAW yace "dukkansu suna nan banda kafadarta" ai abinda akayi sadaka dashi yana ajiye awurin ALLAH, wanda aka cinye kuma ya zama Kashi!

6⃣➖GODIYA GA CHIEF OF THE ARMY STAFF🇳🇬 LAFTANAL JANAR TUKUR BURATAI👏🏻
   Mu al'ummar masarautar BIU BORNO STATE da kewayenta muna godiya ga ALLAH SW da ya azurtamu da Genaral Buhari shugaban kasar 9jr- kuma yadamkawa yaronmu kuma babanmu kuma abin alfaharinmu kuma sanyin idonmu mu mutanen BIU- GENERAL TUKUR BURATAI shugabancin rundunar sojin kasa, tabbas BURATAI Jan gwarzone nagaske, bamuda kamarsa mu 'yan BIU, ALLAH yabashi damanda ya kwato mana garuruwanmu daga hannun boko haram wadanda suka addabi 9jry, kasuwanninmu & wuraren ibadunmu & garuruwanmu lfy, ya kwato mana 'ya'yanmu daga hannun boko haram, kuma yakawo bana babban gagarumin JAMI'A son kowa wacce aka budeta talatannan 30/10/2018 da sauran abubuwan cigaba da yakawo mana na samarda ayyuka da bunkasa yankinmu da ma kasar 9jry gaba,
YA RABBANA! KAYIWA TUKUR BURATAI ALBARKA DUNIYA DA LAHIRA, AMIIIIIIIIIIIIIIIIN

7⃣➖TA'AZIYYA😭‼
   Bazamu taba mantawaba da mummunan ta'addancin BIROM akan al'ummarmu ba musammanma na kashe MAJOR GENERAL IDRIS ALKALI ranar 3/SEPTEMBER/2018-MLDY, suka jefa gawarsa a kogin DURADU suka kuma jefa gawarsa a rijiya agarin GUSHWET yankin SHAN a JOS TA KUDU, wacce aka sami gawar ranar laraba 31/OCTOBER/2018-MLDY,
   Hakika mun zauna nakusan shekaru 2 da IDRIS ALKALI anan BIU kusan shekaru 15 dasuka gabata lokacin yana LAFTANAL KANAL kuma ya dalibtu damu anan masallacin, kuma ya tallafawa al'umma kwarai, kowa ya shaideshi baya sata baya neman mata baya cin hakkin wani ko haram, hatta kiristocinda sukayi aiki dashi sun shaideshi,
👏🏻YA RABBANA! Katsinewa BIROM da duk wanda yakeda hannu a aika aikannan yadda Katsinewa mutanen asabar kuma katarwatsasu kahallakar dasu YA HAYYU YA QAYYUM,
   Muna mika ta'aziyya ga iyalan JANAR ALKALI da mutanen yobe musammanmada rundunar sojin 9jry musamman GENERAL BURATAI bisa wannan babban rashin,
   Lallene zukatanmu suna cikin kuna🖤❣, idanunmu na zubda hawaye😢😭, amma bazamu fadi abinda zai fusata UBANGIJINMU ba, muna bakin cikin rabuwa dakai JANAR ALKALI,
👏🏻👏🏻👏🏻YA RABBANA! KAGAFARTAWA BAWANKA JANAR ALKALI, KAYI MASA RAHAMA, KAZAUNAR DASHI CIKIN ALJANNAR FIRDAUSI,
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻😭👏🏻😭👏🏻😭

via= Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽