MATAKALAN FARLANTA AZUMI

RAMADANA 1442:

(02) : 


MATAKALAN FARLANTA AZUMI:


Ankarbo daga bara'u yace:


Sahabban Annabi (SAW) sun kasance idan mutum yana axumi sai lokacin bude baki ya halarto saiyayi bacci kafin yabude baki to shikenan baxaici komaiba a wannan dare da yininsa har sai wani yammacin, 

Kuma lallai Qaysu da sarmata al'ansariy ya kasance yana da azumi yayinda lokacin bude baki ya halarto saiya zo wurin matarsa yace da ita:

KO AKWAI ABINCI A WURINKI?

sai tace:

A'a babu amma zan fits in nemo maka

To kuma dama ya yini yana aiki sai idonsa yarinjayesa

Sai matarsa ta dawo da taganshi sai tace:

Waiyo shiga uku da yini yakai tsakiya a kashegari saiya suma saiya ambawa annabi (SAW) al'amarinsa sai wannan aya ta sauka :

" AN HALATTA A DAREN AZUMI KU NEMI MATANKU"

sai sukayi farin ciki da ita farin ciki maiyawa

Sai aka sake saukar da wanna ayar:

"KUMA KUCI KU SHA HAR SAI FARIN ZARE YA BAYYANA DAGA BAKIN ZARE"

(bakara: (9).


Abu Habibillah Abdallah Mustapha Assalafiy Biu.