RAMADANA (3)1442 : BY ABDALLAH BN MUSTAFA BIU


Ankarbo daga mu'az Dan jabal (ALLAAH yakara masa yarda) yace:

" ANYIWA SALLAAH SALO GUDA UKU, AZUMI MA ANYI MASA HALAYE GUDA UKU


yakoro hadisin har zuwa inda yace:

AMMA DANGANE DA HALAYYAN AZUMI, TO LALLAI MANZON ALLAAH (SAW) 

( YA TAHO MADINA SAIYA ZAMTO YANA YIN AZUMIN KWANA UKU A KOWANE WATA, KUMA YA AZUMCI RANAR ASHURA, SA'ANNAN LALLAI ALLAAH YA FARLANTA MASA AZUMI SAI ALLAAH YASAUKAR:


" YA KU WADANDA SUKAYI IMANI AN FARLANTA MAKU AZUMI".


SA'ANNAN ALLAAH YASAKE SAUKAR DA WATA AYAR:

" WATAR RAMALANANDA AKA SAUKAR DA ALKUR'ANI ACIKINSA"


SAI ALLAAH YATABBATAR DA AZUMTARSA AKAN MAZUNIN GIDA LAFIYAYYE, YAYI SASSAUCINSA AKAN MARAS LAFIYA DA MATAFIYI, KUMA YATABBATAR DA CIYARWA GA TSOHONDA BAYA IYA DAUKAR AZUMIN, TO WADANNAN WASU HALAYENE GUDA BIYU".


Abu Habibillah Abdallah Mustapha Assalafiy Biu.