KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐15/RABEE'UL-ULA/1440-HJRY
🌐23/NOVEMBER/2018-MLDY

♦TOPIC👉
   [[KAZO BA KOMAI + ZAKA KOMA BA KOMAI]]

   Mutum zai gabato gaban UBANGIJINSA a ranar kiyama shi daya bashida kwandala kamar yadda aka halicceshi a karon farko, bashida komai sai aikinsa kyakkyawa ko mummuna, a wannan ranar salihai zasu sami darajoji a ALJANNA sakamakon kyawawan aikinsu, masu laifi kuma zasu wulakanta acikin ramukan WUTA, ALLAH yakiye,
💡ALLAH SW yace <<kuma dukkansu zasu masa a ranar kiyama dayadaya>> (SRT MRYM-95)
💡ALLAH SW yace <<Hakika tabbas zakuzo mana dayadaya kamar yadda muka halicceku a karon farko kuma kun bar abinda muka kunbar abinda muka mallaka muku a bayan bayayyakinku........ hakika an yayyanke tsakaninku>> (SRT AN'AM-94)   wadannan ayoyi 2 sun tabbatarda komawar mutane zuwa ga ALLAH gaba dayansu ba dukiya ba matsayi ba mukami ba dabara ba karfi,
   Yaku bayin ALLAH! an halicci mutum yazo duniya dayadaya, an marabceshi cikin tsummarda aka lullubeshi, ya rayu wani lokaci a duniya har zuwa mutuwarsa, in ya mutu zai koma ga ALLAH dayadaya yayi ban kwana an lullubeshi cikin tsummar likkafani➖ ALLAHU AKBAR😭, Wannan shine ma'anar <<kunbar abinda muka mallaka muku abayanku>> zai tafi yabar dukiya & mata & 'ya'ya  gidaje benaye & mukami & albashi, yadda ake zare gashi daga kwababben gari, yazowa ALLAH empty sai aikinsa, imma kyawawa- wajen riko da Qur'ani da Hadisi, ko munana- nariko da bidi'a da afkawa haram da sabawa dokokin ALLAH,
➖MEYE SAKAMAKON AYYUKANNAN⁉
💡ALLAH SW yace <<wanda yazo da kyawawan ayyuka yanada sakamakonda yafita alhairi kuma za'a tserar dasu daga firgicen ranar kiyama * wanda kuma yazo da mummuna za'a kifar dasu a WUTA da fuskokinsu, ai ba'a sakayya saida abinda kuka aikata>> (SRT NAMLI 89-90)
   Yaku bayin ALLAH! ba'a batufa a kiyama sai na aiki, shin kanada ayyukanda zaka tsira kuma kayi nasara⁉ infa babu zaka zube warwas a kaskance acikin wuta ko kaine waye❗darajoji a kiyama ba riyal ko dala ko naira bane, kyawawan aikine kawai‼
   Yaku bayin ALLAH! Wani zaka gansa anan duniya miloniyane- a lahira kuma talakane shi bashida lada, Wani kuma anan duniya talakane bashida kudi- amma a lahira miloniyane a lada,
   Don haka yayinda kaga wani yana gasa dakai a motoci da gine gine🏩🏬🏢- kyaleshi kai ka shagaltu da gina lahirarka, ka shagaltu kai da iyalanka wajen karanta Qur'ani da haddaceshi, kaje masallaci da majalisan ilimi da iyalanka, kana bangaren manya, matarka na bangaren mata, yaranka na bangaren yara, bayan la'asar ko magrib ko isha'i, WALLAHI zaku komo gida da manyan tsaunukan lada, domin kowane harafin Qur'ani akwai ladan kyawawa 10, kuma wannan shine hakikanin fadin ALLAH SW 💡<<ku tsare kanku da iyalanku daga wuta>>
   Madalla da wannan kasuwancin, saidai Meyasa mutane ke guje mata⁉
Suna guje matane don basu san kimar kyawawan aikiba, babu wanda yasan kimarsa sai wanda yasan ALLAH, kamar zinarine ba wanda yasan kimarsa sai wanda yasansa, da zaka bawa mai harkan gawayi da ya yar don bai sansaba,
   Don tsananin ranar kiyama- shiyasa mutane ke tsananin bukatar kyawawan aiki, shiyasama karshen maganarda ALLAH yayiwa duniya kamar yadda yazo a littafinsa na karshe (QUR'ANI) wanda bai sake saukarda wani littafi da turo wani ANNABI bayan wannan ANNABIN ba,
Maganarda yau takai samada shekaru 1430, kuma daga kansa babu wata magana sai a lahira👉👉👉
👉💡ALLAH SW yace <<kuji tsoron ranarda za'a komar daku zuwa ga ALLAH sa'annan a sakawa kowace rai abinda ta aikata batareda an zaluncesuba>> (SRT BQR-281)

👏🏻👏🏻👏🏻YA RABBANA KABAMU RAYUWA MAI KYAU A DUNIYA DA LAHIRA KUMA KATSAREMU DAGA AZABAR WUTAAAAA♨♨♨
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via=Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽