KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐25/AL-MUHARRAM/1440-HJRY
🌐05/OCTOBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu

🔸TOPIC👉
   [📩MUHIMMAN WASIKU AKAN SIYASA📩]

➖NA KASASHI GIDA 🔟👉

1⃣➖MUQADDIMA‼
   Biyan bukatar al'umma da kaikawo wajen cimma bukatunsu na alhairi- yana karawa mai shi kusanci da ALLAH da lada gamamme mai yawa

2⃣➖MASHIGA & MATASHIYA‼
   Yadda muka sani wannan makonda ke karewa yau an gudanarda zabubbukan fidda goni a jam'iyyu daban daban a kuma mataki daban daban adukkan 9jry bisa tsarin delget ko kirge, wani wuri an dace da wanda ake so wani wuri kuma ba'a daceba, ALHMDLH ALA KULLI HAAL

3⃣➖📩WASIKA ZUWAGA DELGET NAGARI‼
Kusaurari abinda ALLAH yatanada muku👉
 💡ALLAH SW yace <<wanda yayi silar abu mai kyau yanada kaso acikinta>> [SRT NISA'I-85]
 💡ANNABI SAW "kuyi silar abu mai kyau za'a baku lada, ALLAH zai hukunta bisa harshen ANNABINKU abinda yaso" {BHR}
 💡ANNABI SAW yace "mafi soyuwar mutane awurin ALLAH- wanda yafi amfanarsu, mafi alhairin aiki awurin ALLAH- farin cikinda kashigar azuciyar musulmi, ko kayaye masa damuwa ko bashi ko yunwa, kuma tafiya zuwa ga biyan bukatar musulmi yafi ladan i'itikafi na wata guda kuma zai tabbatarda digadigansa ranarda dugadigai zasu zame, wanda yadanne fushinsa ALLAH yana rufa asirinsa, mugun hali yana bata aiki yadda kunu ke bata zuma" {TDBRNY & IBN ABIDDUNYA}

4⃣➖📩WASIKA ZUWAGA DELGET BARAGURBI‼
Kusaurari sharrinda ALLAH yatanadar muku👉
 💡ALLAH SW yace <<wanda yayi sila mummuna yanada kaso mummuna daga gareta, ALLAH yayiwa komai lokaci>> [SRT NISA'I-85]
 💡ANNABI SAW yace "adu'o'i 3 abin amsawane- adu'ar uba akan dansa & adu'ar matafiyi & adu'ar wanda aka zalunta {AHMD & AB-DWD & TRMZ} DALGET- in baka zabi abinda mutanenka kesoba ka zaluncesu kuma adu'arsu zai fada kanka,
 💡ANNABI SAW yayi mugun adu'a akan mummunar DALGET yace "ya UBANGIJI! duk wanda ya wakilci al'amarin al'ummata yajefasu wahala- kawahalar dashi❗duk wanda yawakilcesu yakaisu ga sauki- kasaukaka masa {MSLM-4669}

5⃣➖DELGET NAGARI KUN SAMI LADA KODA BAKUYI NASARABA‼
 ▪SHEIKH SADHAN yace= wanda yayi sila yanada lada ko ba'a cimma nasaraba domin💡ALLAH SW yace <<wanda yayi sila mai kyau yana kaso>> baice sai YA aiwatuba, hakama 💡ANNABI SAW "kuyi sila zaku sami lada" baice sai ya aiwatuba

6⃣➖📩WASIKA ZUWAGA WADANDA SUKAYI NASARA‼
💡ANNABI SAW yace "cikin mutane akwai mabudan🗝 alhairi makullan🔒 sharri kuma akwai akasin haka, jin dadi ya tabbata ga wanda ALLAH yasa mabudan🗝🗝 alhairai a hannunsa👊, azaba YA tabbata ga wanda ALLAH yasa mabudan🗝🗝sharri a hannunsa" {IBN MJH-237}
   Don haka in kunyi nasara a babban zabe kuzama mabudan alhairi ku inganta rayuwar talakawanku batareda nuna banbanciba, muna tayaku murna da adu'ar dacewa,

7⃣➖📩WASIKA ZUWAGA WADANDA SUKA RASA‼
   Kusani mulki a hannun ALLAH yake yana bawa wanda yaso, kuma duk yawanku 'yan takara dole dayane zaiyi nasara, don haka kuyi hakuri kurungumi kaddarar ALLAH hakan shine alhairi agareku,

8⃣➖📩WASIKA ZUWAGA IYAYE‼
   kurike hannun' ya'yanku zuwaga siyasa mai tsabta- maras zagin ko cin zarafi ko shaye shaye ko Sara suka, 'yan siyasa sun tura 'ya'yansu makaranta da wurin tarbiyya- sunzo kuma suna lalata tarbiyyar 'ya'yanku suyi amfani dasu suci mulki sumore banda ku da 'ya'yannaku, a kiyama kuma ubangiji yajefaku wuta don 'ya'yanku sun lalace❗
   Yakai matashi- shin ka taba ganin wanda yayi bangar siyasa da sara suka ya zama shugaban kasa ko gomna ko chairman ko kansila⁉

9⃣➖📩WASIKA ZUWAGA MAZAJE‼
   Abin bakin ciki da takaici da kaicone kaga matan aure da budurwai- sun sammaka a Kofar dan siyasa koma kagansu har cikin dare dasu ake gararambar siyasa da ihu don tsabar kwadayi da rashin godiya, wata tasha kwaya❗wata ashafa nonuwanta❗ Wata ayi Zina da ita❗Wata a sassareta❗
Jama'a ina mutunci❓ina kunya❓ina kamala❓ina musulunci❓
   yaku mazaje kuzaunarda matanku agidajenku- ranar zabe sufito kujefa kuri'arsu sukoma gida inba hakaba akwai UQUBAR ALLAH‼

🔟➖📩WASIKA ZUWAGA JAGORORIN DUKKAN JAM'IYYU NA KASA‼
   Muna kira da babban murya arika bawa dukkan jihohi damar zaben tantancewa bisa tsarin kato bayan kato ayi irgen zahiri, bawai arika barin wasu gomnoni ko wasu marasa kishi suna mana nadiba❗tunda ba mulkin soja akeba‼
👏🏻YA RABBANA- shugabanninmu nagari katabbatar manasu kuma kakara musu Kuzari, bara gurbinsu kuma kawatsar mana dasu kayi katangar karfe tsakaninsu da MULKI,
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via= Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽