KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE
🌐18/MUHARRAM/1440-HJRY
🌐28/SEPTEMBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu

♦TOPIC 👉
👉DELGET- ALJANNAR ko WUTA♨
👉DELGET- 'YANCIN AL'UMMARKU YANA HANNUNKU✊🏿

NA KASASHI GIDA 6⃣

1⃣➖MUQADDIMA‼
   Musulunci tabada kulawa ga dukkan bangarorin rayuwa, kuma ta umurci kowane mutum yasauke wakilci da nauyin al'umma dake kansa, kuma ta aza laifi ga duk wanda yasaida 'yancin al'ummarsa,

2⃣➖SALIHI NA FIFITA FA'IDAR AL'UMMA AKAN NASA‼
   Musulmi nagari duk inda yasami dama yakan anfani al'ummane kuma yatunkude musu cutuwa, don shima wani tsokane daga al'ummarsa,
 💡ANNABI SAW yace "imanin dayanku baya cika sai yasowa da'uwansa abinda yake sowa kansa"
 💡shiyasama ALLAH SW ya shar'antawa mai karanta SRT FATIHA yin jam'i a adu'oinsa koda shi kadaine=
 =gareka (muke) bauta kuma gareka (muke) neman taimako- maimakon (nake)
 =kashiryar (damu)- maimakon (dani)
 💡shiyasama ANNABI SAW a filin kiyama zai rika cewa= al'ummata❗al'ummata❗

3⃣➖DALGETS- KUSAURARI KIRAN UBANGIJINKU‼
 💡ALLAH SW yace <<kuyi taimakekeniya akan abu mai kyau da taqawa kada kuyi taimakekeniya akan mummunan abu da ta'asa>> [SRT MA'IDA-2]
 ▪IBN-ASHUR- karkashin ayannan- yace= fa'idar taimakekeniya shine saukake aiki da samarda gyara, {AL-TAHREER WAL-TANWEER}
 ▪IBN-KATSEER- karkashin ayannan- yace= ALLAH SW yana umurtan bayinsa muminai da taimakekeniya wajen aikata alhairai da kawarda munanana, yahanasu taimakekeniya akan kawo barna, 💡ANNABI SAW yace "kataimaki dan'uwanka azzalumi- taimakonsa shine kahanashi zalunci" [AHMD, BHR, MLM] 💡kuma ANNABI SAW yace "wanda yayi silar alhairi yanada lada irinna wanda ya aikata" [MSND BZR & KASHFUL ASTR]
{TAFSIRU IBN KATHEER}

4⃣➖WAKILCI AMANACE‼AMANA KUMA BABBAN ABUNE‼
   Yaku wakilai (DALGET) cin amanar al'ummarku cin amanar ALLAH ne,
 💡ALLAH SW yace <<lalle ALLAH yana umurtanku kumayarda amana ga masu ita>> [SRT NISA'I-58]
 💡ALLAH SW yace <<mun bijiro da amanoni wa sama da kasa da duwatsu sai suka ki dauka sai mutum yadauka, lalleshi mai yawan zaluncine da yawan jahilci, domin ALLAH ya azabtarda munafukai..... >> [SRT AHZB-72-73]

5⃣➖DALGET- IN KUNYI MAI KYAU KUNYIWA KANKU❗HAKAMA IN KUN MUNANA‼
 💡ANNABI SAW yace "idan akazo tsallake siradi a kiyama za'a turo amana da zumunci su tsaya a hagu da daman siradi" wasu zasu wuce kamar walkiya,................ Wasu kuma zasu kasa wucewa" [MLM]
 💡ANNABI SAW yace "duk wanda ALLAH yawakiltashi akan wasu yamutu yana mai ha'intarsu sai ALLAH ya haramta masa ALJANNA"

6⃣➖KIRA GA WAKILAI (DALGET)
  Yaku Wakilai masu zaben fidda gwani- daga jihohin👉 Adamawa 👉Benue 👉Delta 👉Ebonyi 👉Enugu 👉Gombe 👉Jigawa 👉Kaduna 👉Katsina 👉Kebbi 👉Kogi 👉Kwara 👉Nasarawa 👉Oyo 👉Plateau 👉Rivers 👉Sokoto 👉da jihata Borno
➖kuguji cutarda al'ummanku wajen zabo musu barayi, azzalumai, mayaudara, madamfara wadanda zasu azabtar dasu na shekaru 4😢
➖kuzabo musu kishinsu, masu kare martabarsu, masu inganta musu makarantu da ilimi da samar musu aikin yi❗masu inganta musu asibitocinsu da lafiyarsu❗masu inganta musu ruwan sha & lantarki & hanyoyi❗uwa uba masu taimakawa addinin ALLAH❗
➖Wanda yake kwatantawa ku tabbatar dashi❗Wanda bayayi kuyi waje dashi don ba gadon gidansu bane‼
👊kuyi amfani da damanku ku hana dukkan azzalumi kaiwa ga nasara koda najikinkune‼
👊kuyi amfani da damanku nabawa adali dama koda na nesa dakune‼
=da hakane ku da iyayenku da iyalanku da 'ya'yanku da kannenku da jikokinku rayuwarku zai inganta😊
Kusani shekara 4 ba kwana 4 bane,

➖DALGET= in kun ha'incemu mu al'ummarku ALLAH YA ISA😭😭😭
KUMA SAI ALLAH YA TAMBAYEKU‼‼

👏🏻YA RABBANA KABAMU SHUWAGABANNI NA KWARAI ADILAI👏🏻
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via= Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽