KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐06/ZUL-HIJJA/1439-HJRY
🌐17/AUGUST/2018-MLDY

🎤MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu

🛑TOPIC👉
 [[AZUMIN ARAFAN BANA 1439 - TA MUSAMMANCE]]

NA KASASHI GIDA 🔟

1⃣➖MUQADDIMA‼
   Yaku bayin ALLAH! muji tsoron ALLAH kuma mugode masa akan ni'imarda yayi mana na shar'anta mana layya da dabbobin gida🐪🐂🐑🐐, ba da dabbobin daji🐅🐆🐘🦏 ba kuma ba da dan Adam ba, ya saukaka tane don musami kusanci da ubangijin, kufiddo da kudadenku masu kima kusayi abin LAYYA, an shar'antata shekara ta 2 da hijira,

2⃣➖HUKUNCIN LAYYA‼
 ◼MALAMAI sun kasu 2 akai=
 (1) WAJIBINE➖shine maganar AUZA'IY & LAITH & mazhabin ABU-HANEEFA kuma dayace daga ruwayar AHMD kuma shine zahirin maganganu 2 na mazhabin MALIK,
 (2) SUNNACE MAI KARFI➖shine maganar JAMHUR & SHAFI'IY & dayan maganar MALIK, amma yawancin masu wannan fahimtar sunce barinta haramunne ga wanda yakeda ikon yi,
Mai JAWAHIRUL-IKLIL sharhin (MUKHTASAR) ya ambato= idan 'yan gari guda sun bar LAYYA to za'a yakesu domin tana cikin SHA'AIRUL ISLAM,
 ◼IBN TAIMIYYAH yace= abinda yafi bayyana yin LAYYA ga mai iko wajibine, domin tana cikin mafi girman SHA'AIRUL ISLAM na dukkan duniya kuma ibadace aka hadeta da salla kuma tana cikin millar IBRAHIM da aka umurcemu mubisa kuma nassoshi sunzo da umurnin yinta kuma ba'a sami nassinda takore ba,  dubi {MAJMU'UL FATAWA LI'IBNIL QASIM- MJLD 32 SHAFI'IY 162-164 & SHARHU MUWATDA LIL UTHAIMEEN MJLD 3}

3⃣➖HIKIMAR SHAR'ANTATA‼
   An shar'anta LAYYA don raya anbaton IBRAHIM KHALEELULLAH,
💡ALLAH SW yace <<mun fansheshi da abin yanka mai girma * said muka wanzarda ambatonsa a mutanen karshe>>
   Daga hikimarta akwai wadata iyali da al'umma da nama,
💡ANNABI SAW yace <<ita ranakune na ci da sha da ambabaton ALLAH>>

4⃣➖LAYYA DA DANDAKAKKE‼
💡ANNABI SAW yayi LAYYA da raguna 2 - - - - dandakakku {AHMD} kuma yayi da wanda ba'a dandakeba,

5⃣➖SHARUDDAN LAYYA 2‼
 (1) dolena dabbar takai minzalin layya ➖rakuma🐪 sai takai shekaru 5 ➖shanu🐃 shekaru 2 ➖ akuyoyi🐐 shekara 1 ➖raguna🐑 wata 6
 (2) yakubuta daga aibin gurgunta & makanta & rashin lafiya & kanjama {MALIK & TRMZ & NASA'I}

6⃣➖LAYYAR HUFRAH‼
 ◼SHEIKH SALIH UTHAIMEEN yace= wasu in mamacinsu yamutu shekarar farko sukan yanka masa LAYYA suna masa taken LAYYAR HUFRAH suna kebenceshi ga mamacin, wannan bidi'ace batada asali,

7⃣➖DAGA LADUBBAN YANKA‼
 ◼UTHAIMEEN yace= wanda zai iya anfison yayanka da hannunsa, wanda bazai iyaba sai wani yayanka masa amma anfison yahalarci wurin yankar kuma mai yankan yayi bismilla ya ambaci sunansa, in bai ambaci sunanbama yayi domin 💡ANNABI SAW yace <<kowane aiki tareda niyyarsa>> amma anfison ya ambaci sunan,
   Wasu kuma yayinda zasu ambaci sunan sai sure shafa bayan dabbar da fuskarsa- bidi'ace,

8⃣➖KAIFIYYAR YANKAR‼
 ◼UTHAIMEEN yace= dukkan wuya daga samanta zuwa kasanta wurin yankane, saidai ga rakumi🐪 anfison a soke kasar wuyarsa cikin kororonda take dafda kirjinsa, shanu da tumaki da awaki🐃🐑🐐 kuma anfison a yankasu a saman wuya dafda kai, amma dukkansu in an soke ko aka yanka a tsakiyar wuya yayi,
 ◼kuma UTHAIMEEN yace= duk wanda yayanka dabbar wani a LAYYAR ya dauka nasane sai yagane ba nasaba to LAYYAR ya tabbatane ga mai asalin dabbar ba ga wanda ya yankanba domin shi tamkar wakiline,

9⃣➖AZUMIN ARAFAR BANA SPECIAL CE‼
💡ANNABI SAW yace <<azumin ranar ARAFA yana kankare zunubin shekararda yawuce da kuma mai zuwa, azumin litinin kuma shine ranarda aka haifeni acikinsa kuma aka turoni acikinsa kuma aka mini wahayi acikinsa>> {MSLM}
   ARAFAN bana na 1439-HJRY zai kasance ranar LITININ, don haka muyisa da niyyar yinin ARAFA da kuma LITININ zaka sami darajoji guda 4=
 ¹➖kankare zunubban shekaru 2
 ²➖raya ranar haihuwar ANNABI SAW
 ³➖raya ranar turo ANNABI SAW
 ⁴➖raya ranar farkon saukan wahayi ga ANNABI SAW


🔟➖TA'AZIYYA😭 & ADU'A👏🏻‼
😭😭😭muna mika ta'aziyyarmu ga mu musulman duniya da ma zurriyyarmu anan gaba➖bias rasuwar babban SHEHI RABBANY kuma farkon wanda yabada shawarar kafa Jami'ar Musulunci TA MADINA da kuma kafa kungiyar RABIDATUL ALAMUL ISLAM da kuma kafa IZA'ATUL QUR'AN kuma ya rubuta dimbin litattafai daga cikin kawai (MINHAJUL-MUSLIM) da kuma (HAZAL-HABEEB-MUHAMMAD RASULULLAHI SAW-YA MUHIBBU)
wanda yarasu talata 3/ZUL-HIJJA/1439-HJRY ➖14/AUGUST/2018-MLDY➖SHEIK ABUBAKAR JABIR ALJAZA'IRY😭😭😭
👏🏻👏🏻👏🏻YA RABBANA YADDA SHEIKH YABADA GUDUMAWA YA RUBUTA TARIHIN HABIBINKA SAW MAI SUNA (HAZAL-HABEEB) to KAHADAMU DASHI TAREDA HABIBINNAKA A JANNATUL FIRDAUSI👏🏻👏🏻👏🏻
AMIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via👉 Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽