KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐20/ZUL-HIJJA/1439-HJRY
🌐31/AUGUST/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu

⭕TOPIC👉 [[HATTARA DAI MATASHI]]

NA KASASHI GIDA👉  6⃣

1⃣👉 MUQADDIMA‼
  ◼IBNUL QAYYIM yana cewa= sakacin yiwa kai hisabi da kuma biyewa abinda zuciya keso— suna hallakarda zuciya🖤
  💡ANNABI SAW yace "jarumi shine wanda yake yiwa kansa hisabi kuma yake aiki don abinda ke bayan mutuwa, malalaci kuma shine wanda yabi son zuciyarsa yayita buri akan ALLAH"

2⃣👉 MATASA DA ZAMANI‼
   Lalle lokaci⌚ ba'a iya sayanshi da kudi don haka asararshi yafi mutuwa girma, don in ya wuce bazai dawoba,
   Lokacin samarta zangone mai albarka, cikinta akwai karsashi da karfi da mora, acikinta ake gina daukaka kuma ake sadaukarwa, domin gaban MATASHI akwai tunkarar addini, gida, iyali, zurriya da kalubalen dny & lhr, ba abinda yafi dacewa MATASHI yamori rayuwarsa dashi samada bautan ALLAH,
 💡shiyasa ANNABI SAW yasa MATASHINDA yataso da ibada cikin mutum 7 dake inuwar ALLAH agobe kiyama,

3⃣👉 SABUBBAN LALACEWAR MATASA‼
   Muhimmansa= munin gidanda yafito/ munin abokai/ munin society➖ Sai suhaifar masa shaye shaye & zina & luwadi & Zaman kashe wando & yawon banza & ta'asa,

4⃣👉 RUDIN SAMARTAKA‼
   Yakai MATASHI! kaguji rudinda SAMARTA kema kamar haka👉
Ai lokacinkane❗Kasheke ayarka❗kafantama❗kahole❗kayi iskancinka❗kabar salla❗kanada sauran lokaci da kuma damanda zaka tuba nan gaba kagyara❗
SUBHANALLAH‼😭 wannan rudin WALLAHI yafi makami mai linzami fatattaka rayuwa💔‼

5⃣👉 MATASHI RUDADDE KAFARKAFA‼
   Saurari kiran MAHALICCINKA👉
 💡ALLAH SW yace <<yaku mutane- lalle alkawarin ALLAH gaskiyane kada rayuwar duniya da mai rudarwa su rudeku♦lalle shedan makiyine agareku kurikeshi makiyi domin yana zuga tawagarsa suzama 'yan wutar sa'ir>> {ST ZUMAR 5-6}
 💡ALLAH SW ya hikaito mana amsar 'yan aljanna ga 'yan wuta yayinda suka nemi agajinsu <<kun fitini kanku kukayita jan kafa da mugun fata kuma kukayita kokonto kuma buri yarudeku har al' amarin ALLAH yazo, kuma mai rudarwa yarudeku♦a yau baza'a karbi fansa daga garekuba ko daga kafiraiba, makomarku jahannamace, tir da wannan makoman>> {SRT HADID 14-15}
MATASA nawa akayi masu iskanci ana tallata masa tuba ana binsa dashi yayita cewa tukuna, ya dauka bazai mutuba sai iyayensa da kakanninsa sun mutu, ya dauka bazai mutuba sai ya tsufa tsukuf, ya dauka bazai mutuba sai yayi jinya sosai➖
kwatsam sai ajali tayi masa bazata yamutu ba tubarda yake sha'awa⁉

6⃣👉 MUTUWA AJALINE➖BA JINYA KO TSUFABA‼
   Shekaru kadan dasuka shude in kaga anyi mutuwa dayan biyune ko maras lafiya ko dattijo tsukuf, matshi ko lafiyayye da wuya yamutu,
   Amma a yanzu an wayi gari mutuwar lafiyayyen natashi na bazata tafi yawa samada mutuwar dattijai da marasa lafiya yawa, hatsarin mota na kisa hakama cutar suga da hawan jini da bugun zuciya da sida da cututtuka marasa kan gado wadanda kakanninmu basu sansuba, ba komai yakawosu face zunubbanda mukeyi kakanninmu basuyiba,
♨mun wayi gari ayau MATASA sunfi dattawa mutuwa😭
♨lafiyayyu sunfi masu cututtuka kwance akan gado mutuwa😭
   📢Don haka wajibine ga musulmi yagaggauta tuba, in SAURAYINE yayi amfani da damansa yabautawa ALLAH kafin kuruciyar tawuce, in kuma lafiyayyene yayi amfani da lafiyar kafin jinya yazo masa, domin yadda yaga wasu na fama da jinya watarana shimafa akansa❗

👏🏻YA RABBANA KABAMU RAYUWA MAI KYAU A DUNIYA DA LAHIRA KUMA KATSAREMU DAGA AZABAR WUTAAAAA♨
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via= Abubakar BN MUSTAFA BIU✍🏽