KHUDUBAR MASJID MIYETTI- BOLARI- GOMBE STATE:

🌐21/RABEE'UL-ULA/1440-HJRY
🌐30/NOVEMBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu

♦TOPIC👉 (MU JADDADA IMANINMU)

   Kuma ara mini jinku da hankulanku don sabunta IMANINMU, don muhimmancin IMANI ALLAH yasaukarda sababinta azuciyar muminai,
💡ALLAH SW yace <<shine yashigarda nutsuwa azukatan muminai domin sukara imani tareda imaninsu>> {SRT FATHI} kuma ya horemu daga rashin imani don bushewar zuciya👉
💡ALLAH SW yace <<shin lokaci baiyi bane ga masu imani zuciyarsu yayi khushu'i don ambaton ALLAH? kada su kasance kamar wadanda aka bawa littafi bayan dogon lokaci zukatansu yabushe yawancinsu suka zama fasikai>> {SRT HADID-16} kunga ya siffanta zuciyarsu ba imani da bushewa & yahudanci & nasaranci & fasikanci,
   IMANI da TAQAWA yafi triliyoyin naira & royal & dollars & dinari, kai yafima duniya gaba daya, shiyasama ANNABI SAW yafi kowa samun kaso mafi tsoka cikin haka👉
💡ANNABI SAW yace "na fiku tsoron ALLAH" (BHR-5063 & MSLM-1401)
💡ANNABI SAW yace "da kunsan abinda nasani da kunyi dariya kadan kuma kuyi kuka dayawa" sai SAHABBAI R/A suka tsugunarda kansu sai kuka, (BHR-4621 & MSLM-2359)
💡ANNABI SAW yace "ta yaya zanji dadi alhali Mala'ika yasa bakin kaho abakinsa ya cika kumatunsa da iska yana jiran abashi izinin busa" (AHMD & TRMZ)
🔊IBN UMAR R/A- ance dashi shin SAHABBAI suna dariya? Sai yace= Eh, ammafa IMANI azukatansu kamar tsaunuka, (HILYATUL AULIYA)
🔊ABDLH IBN AMIR yace= naga UMAR R/A yace dibi damka na kasa yana cewa= kaitona da ba'a yiniba, da mahaifiyata bata haifeniba😭
🔊MU'AZ IBN JABAL yace= ina neman tsarin ALLAH daga darenda safiyarta zuwa WUTA♨
🔉SUFYAN AL-TSAURY yana kan shimfidar mutuwa sai HAMAD yace dashi= albishirinka ya baban ABDLH, zaka fuskanci ALLAH wanda kake kaunarsa kuma shine mafi jinkan masu jinkai,
SUFYAN yafashe da kuka yake cewa= don ALLAH ya HAMMAD, shin kana ganin irina zai tsira daga wuta⁉
🔉RABEE'U IBN KHAITSAM- in ance masa- ya kawayi gari? Sai yace= mai rauni mai laifi ina cinye arzikina ina jiran ajalina😢
🔉UWAISUL QARNY- in ance dashi- ka wayi gari lafiya? Sai yace= ina lafiya ga mutuminda in yayini baida tabbacin wayewar gari, hakama inya wayi gari bashida tabbacin yini,
🔉IMAM SHAFI'IY yanakan shimfidar mutuwa- akace dashi- ya kawayi gari? Sai yace= na wayi gari mai barin duniya! mai rabuwa da 'yan uwa! mai barin aiki! mai haduwa da aikinsa! mai kwankwadar kofin mutuwa! mai zuwa wurin ALLAH! Sai yafashe da kuka yace= ban saniba raina ALJANNA zataje- in tayata murna, ko zuwa Wuta- in mata jaje‼
🔉MALIK IBN DINAR yakanyi salla bayan ya idar sai yadamke gemunsa yana kuka yana cewa= nasan ALJANNA nasan WUTA- saidai bansan a wanne gidajen 2 za'a saukeni ni MALIK ba😢
🔉WAHAB IBN MUNABBIH yace= ANNABI ADAM A/S bayan cin itacenda aka hanashin yayi shekaru 300 yana kuka kuma baya iya daga kansa yakalli sama‼
🔉ABU DARDA'I yace= anajin karar shishshikar kuka cikin kirjin ANNABI IBRAHIM A/S
🔉Hakama anajin karar shishshikar kuka cikin kirjin ANNABI MUHAMMAD SAW,
   Yakai masoyi mai hankali! duniyafa gubace mai kisa, zukata sun gafala daga kaidinta, zuciyarka zuciyace mai rauni, aikinka aikine mai rauni,
   Yakai Miskini irina! Shin kana tunanin inane makonarka⁉ya mai cin riba da rashawa- cewa kanka inane makomarka⁉ya mai kisan mutane- cewa kanka inane makomarka⁉ya mai zina da luwadi da tsafi- cewa kanka inane makomarka⁉
♨😢SUBHANALLAH! ga kanan gaban ALLAH tsirara ba takalmi- yana ce maka 💡<<kakaranta littafinka da kanka ayau ya isheka hisabi>> a wannan ranar <<duk wanda ya aikata aikin alhairi ko sharri kamar kwayar zarra zai ganshi>> kuji tsoron wuta bayin ALLAH! Wallahi zafinta tanada tsanani! zurfinta da nisa! Abincinta Wuta❗abin shanta wuta❗Tufarta wuta❗shimfudarta wuta❗yanada gudumar wuta❗gudumarta wuta❗
😢in sun nemi abinci= GISLIN & ZAQUM & DWARI'IN♨
😢in sun nemi ruwa= tafasashsen rubabben mugunya mai tsitstsinka hanji♨
😢in sun nemi sassauci= za'ace kudandana babu abinda zamu kara muku saidai azaba♨
😢in yanemi fita= za'a mayar dashi cikinta♨
😢in yanemi mutuwa= za'ace kudawwama acikinta♨
CI & SHA & TUFA & MAYAFI & SHIMFIDA & NISHI & SHAQA duk WUTAAA♨‼

Shin wannan yafi alhairi ko kuma ALJANNAR DAWWAMA da akayiwa mai taqawa⁉
👏🏻YA RABBANA KABAMU RAYUWA MAI KYAU A DUNIYA DA LAHIRA KUMA KATSAREMU DAGA AZABAR WUTAAAAA👏🏻
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻
via= Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽