KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐21/R-TSANI/1440HJRY
🌐28/DECEMBER/2018MLDY

🎙MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu

⭕TOPIC👉
  [[FARKON DAREN QABARI]]

➖NA KASASHI GIDA 7⃣

1⃣➖MUQADDIMA‼
   Yaku bayin ALLAH! Mutuwa hakikace da kowa zai kwankwadeta, Rayuwa kuma kasuwace ta sayan guzuri na alhairi ko sharri, Mai hankali shine wanda yayi aiki mai kyau don lahirarsa, yarabu da duniya da karancin nauyin zunubi,

2⃣➖TATTALI‼
   Yaku bayin ALLAH! Lalle ambaton mutuwa da QABARI da firgicenta yasa Malamai da masu taqawa kuka musammanma yayinda suka tunada DARENSU NA FARKO cikin QABARI da kadaici da canjin halayya kuma da kaucewa mummunar makoma, shiyasa suka gaggauta ayyuka nakwarai don samun kyakkyawar makoma,

3⃣➖FARKON DARENKA DA ALLAH‼
   Farkon DARENKA da ALLAH shine a QABARI, dare biyune ke zama a tunanin mutum= ¹ darenda kake gidanka tareda iyalanka da yaranka da dangi kuna kallo da ciye ciye cikin ni'imar rayuwa da dariya da walwala, ² darenda yabiyo wannan daren kwatsam mutuwa ya daukaka an bizneka a QABARI, Farkon lokaci Farkon darenka aciki😢, YACE👉
 HMMMMMMMM! nabar wuri zuwa wani wuri❗natafi daga wurin kwanciyana adakina zuwa wani daki daban❗barci ya kauracewa idona, ALLAHU AKBAR❗ya DAREN FARKO zai kasance mana a QABARI⁉yayinda za'a sanya mutum daga shi ba komai sai aikinsa, ba mata❗ba yaro❗ba abokin sana'a ko na hira,
💡ALLAH SW yace <<sa'annan za'a mayar dasu ga ALLAH majibincinsu na gaskiya >> {SRT AN'AM=62}

4⃣➖FARKON DARE A QABARI‼
   FARKON DARE A QABARI- yasa mutane dayawa kuka- malamai da mahukunta, mawaka dayawa sun wake alhininta, an wallafa dimbin littafai akansa,
ALLAHU AKBAR❗shine ranarda katifa da filonka kasake! Slin shine itatuwa ko tukwane! Rufi shine kasa! Mayafi shine likkafani! Zai tattauna da muhawara Munkarun da Nakirun,

5⃣➖MAMACI BAZAI DAWOBA DUK NACI‼
 ◼Anzo da wani bawan ALLAH salihi wanda yake cikin magagin mutuwa sakamakon cizonda maciji yayi masa lokacinda yafita bulaguro kuma ya manta baiyi sallama da iyayensaba- numfashinsa sama sama yana cewa= yaya zan rabu da 'ya'yana akaramin lokaci haka batareda na gansuba⁉banfa yi sallama da iyayenaba⁉haka rayuwa zata mini tasa sabani tsakaninmu⁉haka zan rabu da dukkan dukiyata akaramin lokaci⁉ZUWA QABARI gidan kadaici⁉
YA kai miskini irina➖shin ka taba tunanin haka ga rayuwarka⁉
 ◼ALHASAN IBN HASAN yayi mutuwar bazata sai matarsa tafita da 'ya'yanta ta buga bukka agefen QABARINSA, don bakin cikin mutuwar tayi rantsuwar ita da 'ya'yanta zasuyi kuka har tsawon shekara anan, da shekarar tacika cikin dare ta tattare bukkar zata tafi tareda 'ya'yanta sai wani tambayar wani batareda tana ganinsuba=
Shin sun sami abinda suka rasa⁉
Sai aka amsa masa= a'a sun yanke tsammani sun koma batareda sun sami abinda suka rasaba, batareda an mayar musu ajiyarsuba‼
‼ALLAHU AKBAR‼nacinsu baisa gawar yayi musu maganaba, bai taba fitowa wurinsa yayi hira dasu koda na dare dayaba, bai sumbaci yaransaba, baiga santaleliyar matarsaba, kunji farkon dare a QABARI‼
   Saidai akwai ranaku alahira, in ya kyautata aiki suma sun kyautata to zasuyi madawwamiyar rayuwa tare a ALJANNA,
💡ALLAH SW yace <<kuma wadanda sukayi Imani kuma zurriyyarsu suka bisu da imani zamu hadasu dasu (cikin ALJANNA) bazamu rage musu komai daga aikinsuba>> {SRT TDUR=21}

6⃣➖UMAR BN ABDIL-AZIZ YANA TUNA FARKON DARENSA A QABARI‼
 ◼Babban Malami IBN ZIYAD yacewa UMAR IBN ABDUL'AZIZ= ya AMEERAL MUMININA- Kafin kahau mulki a MAKKA kana cikin ni'ima da lafiya da walwala, yanzu kuma bayan hawanka mulki me yacanzaka haka ka rame ka kode⁉
 Sai UMAR yace dashi= hmmmmmmmm! Ina tuna farkon shigana QABARINE, yaya zaka ganni aranarda za'a kwabe mini tufafina😢 akaini QABARI inyi filo da kasa😢 na rabu da masoya😢 na bar abokai😢 bayan kwanaki 3 in ka ganni cikin QABARIN sai ka firgita😢‼
 ➖Ana Sakai QABARI dan'uwa daga ranar gawarka ta fara kumbura😢 kwana kadan idanunka sun zazzaro😢 tumbinka ya fashe😢 doyi da wari yacika QABARIN😢 tsutsa sun lullubeka😢 ba kyan gani😭😭😭

7⃣➖RUFEWA‼
   Yaku bayin ALLAH! Munzo karshen hudubar mai taken DARENKA NA FARKO CIKIN QABARI, ina neman kowannenmu yatanadi haskensa don haskaka FARKON DAREN QABARINSA, WALLAHI ba abinda zai haskaka QABARI sai imani da kyawawan ayyuka, mu gabatarwa kanmu abinda zai tayamu hira a QABARI, ranarda za'a rabamu da iyalai da dukiya da 'ya'ya da abokai da motoci da waya da talabijin da kudi da man komai‼
👏😢YA RABBANA KAHASKAKA MANA QABARINMU! KAWADATAMU ACIKINTA DA ABOKIN HIRA NAGARI ACIKINTA! KABAMU BARCI ACIKINTA, DA ALJANNA IN MUN TASHI DAGA GARETA,
AMIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIN👏😢👏😢👏

via👉 Abubakar BN Mustafa Biu✍