KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐17/SAFAR/1440-HJRY
🌐26/OCTOBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA= Abubakar BN Mustafa Biu

🔸TOPIC=
  [[DAGA MAS'ALOLIN ZAMANI]]
  FITOWA NA➖2⃣

NA KASASHI GIDA 7⃣

1⃣➖MUQADDIMA‼
   Idan Baku mantaba makonda yagabata akan wannan mimbarin munyi khuduba mai taken [[MAS'ALOLIN ZAMANI- FITOWA NA 1⃣]] munyi bayanin tsarki da tururi & salla daukeda najasa a kwalba & bada jini & cire gaba daga mamaci zuwaga rayayye & aiki da na'urar amsa kuwwa & sanya gawa a firiji,
   Yau kuma insha'allahu zamu cigaba akanta da taken [[MAS'ALOLIN ZAMANI- FITOWA NA 2⃣]]

2⃣➖YANKA DA NA'URA MAI SARRAFA KANSA‼
 ▪DR ABDLH BN ABDUL'AZIZ JIBRIN yace👉 idan ana yanka da na'ura mai sarrafa kansa (automatically) wacce take iya yanka dabbobi dayawa alokaci daya- ya halatta in mai sarrafawar yayi bismilla yayinda zai kunna na'urar yankar, saidai in zai yankasu rukuni rukunine to zaiyi bismilla yayinda kunnawa don yanka kowace rukunin,
   Sa'annan bai halatta wani yayi bismillan wani daban kuma yakunna na'urar yankar ba, kuma wajibine wanda zai kunnan yazanto cikin wanda ya halatta aci yankarsu,
   Sa'annan takaituwarda wasu keyi nasanya wata na'urarda zata rika maimaita bismilla ko kuma rubuta bismillan ajikin wukar yankar baya halatta yankar domin mai yankar baiyi bismilla ba,
(FATAWA LUJNATUD DA'IMAH & TAUSIYYATU MAJMA'IL FIQHIL ISLAMY BI JIDDA & BI SUDAN & FIQHUN NAWAZIL- DR MUHD JIZANY & SHARHUL MUMTI'I & SHARHU UMDATIL FIQH)

3⃣➖SALLAR KUSUFI YAYIN GAJIMARE‼
   Tun cikin Qarni masu yawa abaya MALAMAI sun tabbatarda ana iya gane lokacin kisfewar Rana☀ ko Wata🌙 tun kafin lokacin don ganin wasu alamu sanannu, hakan baya cikin da'awar sanin gaibu, amma anfison kada abada labarinsa sai ya auku don ganinsa kwatsam yafi tasirin girgiza zuciya,
   Amma idan FALAKIYYUN suka bada labarin haka to ba'a sallar KHUSUFI kafin lokacin saidai in anga aukuwarta, hakama wadanda basu gani agarinsuba ko hadari ya hanasu gani- to su ba'a shar'anta musu sallar KHUSUFI ba don basu gantaba,
(FATAWA UTHAIMEEN & SHARHU UMDATIL FIQH)

4⃣➖KIRAN SALLA A RADIO KO TALABIJIN‼
 💡ANNABI SAW yace "idan kunji kiran salla kurika fadin abinda ladanin yake fada" [BHR-611 & MSLM-383]
   Idan mutum yaji kiran salla a radiyo📟 ko talabijin📺 kuma yazanto (LIVE) wato kai tsayene ladanin yake kira alokacin kuma lokacin sallar yayi to an shar'anta masa amsawa da kuma adu'o'in bayan kiran, in kuma ba LIVE bane recording akayi to ba'a shar'anta masa amsawaba,
(FATAWA BN BAZ & FATAWA UTHAIMEEN & SHARHU UMDATIL FIQH)

5⃣➖DASHEN MARAINA‼
   Cire marainar wani don dasawa wanda baida maraina haramunne, domin kwayoyin halittarda ke zantowa cikin maniyyi yana zantowane cikin marainar namiji tun lokacinda aka haifeshi yana jariri, don haka in an dauki na wani aka sawa wani tamkar adauki maniyyin mai haihuwa asawa matar wani da baya haihuwa- kaga in tasami ciki yazanto cikin shegene ba gado, shiyasa ijma'in malamai suka haramta,
(SHARHU UMDATIL FIQH)

6⃣➖JUYA ABIN ZAKKA‼
   Bai halatta mai bada zakka ko kuma komiti mai tara zakka da rabawa sujuya dukiyar zakka ta kasuwanciba kafin bawa mabukataba, don hakan yana kawo tsaiko ga gaggautawa tareda cutarwa ga wanda za'a bashi,
(MAJ'MA'UL FIQHY BI RABADATIL ALAMIL ISLAMY BI MAKKA & FATAWAL LUJNATUD DA'IMAH & FATAWA BN BAZ & FATAWA UTHAIMEEN & SHARHU UMDATIL FIQH)

7⃣➖MATARDA MIJINTA YABACE‼
 ▪UMAR BN KHATDAB R/A yace👉 zata jira shekaru 4 sai  tayi takaba,
 ▪IBNUL MUSAYYIB yace👉 wanda yabace awurin yaki matarsa zata jira shekara daya,
 ▪IMAM MALIKAL cikin daya daga ruwayarsa yace👉 zata jira gorgodon yadda mai nasara a yaki da wanda akayi nasara akansa zai dawo,
 ▪SHEIKH DR ABDLH JIBRIN yace👉 a wannan zamaninda yake cikeda hanyoyin sadarwa na zamani da social media da yawaituwar hanyoyin cigiya harma duniya yazanto kamar gari guda➖ ya dace Alkalai surage tsawon lokacin jiran wanda yabata, surika la'akkari da wuri da yanayi da zamani da halinda mutum yabata sai suyi hukunci gwargwadonta,
(MAJMU'UL FATAWA & SHARHUL MUMTI'I & SHARHU UMDATIL FIQH)
   Gaskiya yanada muhimmanci lura da wannan tunda za'a iya bada cigiya ta Facebook da What's up da ire irensu, musammanma a wannan zamani dake cikeda fitintinun karnukan maza masu farautar mata su lalatasu, jiran shekaru 4 ba miji jidaline, tunda shi ANNABI SAW bai kayyade shekaruba

👏🏻YA RABBANA KABAMU RAYUWA MAI KYAU A DUNIYA DA LAHIRA KUMA KATSAREMU DAGA AZABAR WUTAAAAA!
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via= Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽