KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐10/SAFAR/1440-HJRY
🌐19/OCTOBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu

🔸TOPIC👉
  [[DAGA MAS'ALOLIN ZAMANI]]
   FITOWA NA➖ 1⃣

NA KASASHI GIDA 7⃣

1⃣👉 MUQADDIMA✔
   Lalle Malaman al'ummannan bada dukkan kwazonsu suka keda wahalhalu masu yawa wajen neman ilimin addini = sa'annan basuyi kasa agwiwaba wajen irin hakaba wurin yada ilimin ga dalibai, wajen karantarwa da rubutawa don anfanarda 'yan baya,

2⃣👉 WANKE TUFA DA TURURI✔
   ALLAH SW ya halicci ruwa mai tsarkine don tsarkake babbar najasa da karamarta,
💡ALLAH SW yace <<yana saukarda ruwa daga samene don yatsarkakeku>> {SRT ANFAL-11}
💡ALLAH yace <<in baku sami ruwaba kuyi taimama>> {SRT MA'IDA-6}
   Wadannan suna cikin hujjojin wadanda ke cewa ba'a tsarkake najasa saida ruwa, da kuma Hadisinda ANNABI SAW yayi umurnin zuba gugan ruwa akan fitsarinda akayi a masallacinsa, (BHR & MSLM)
   Wasu Malamai kuma suna ganin idan an gusarda najasa da ruwa ko rana ko iska ko kasa ko kyalle ko tururi muddin ya gusarda najasar to ya tsarkaka,
▪SHEIKH UTHAIMEEN shima ya rinjayarda hakan, domin Hadisinda yanuna najasar takalmi ko tufar mata in yaja najasa daga baya yaja kasa mai tsarki yakawar dashi to ya tsarkaka, da Hadisin tsarki da foge,
[SHARHU UMDATUL FIQH & SHARHUL MUMTI'I & NAILUL AUTDAR & IGATSATUL LAHFAN & MAJMU'UL FATAWA & BIDAYATUL MUJTAHID & FATHUL BARY]

3⃣➖SALLA DAUKE DA NAJASA A KWALBA❌
   Idan mutum yadibi fitsari ko bayan gida ko jinin haila yazuba acikin kwalba🍾 don kaiwa gwaji sai yayi salla da ita a aljihunsa, to sallarsa bata ingantaba,
[MAJMU'U FATAWA UTHAIMEEN & SHARHUL MUMTI'I & SHARHU UMDATIL FIQH]

4⃣➖BAYARDA KARIN JINI✔
   Ya halatta adibi nagartaccen jinin lafitayye akarawa maras lafiya amma da sharadin wanda za'a debi jininnasa ya mallaki hankalinsa kuma bazai cutuba, ammafa dolene yazanto kyauta ba da kudiba, domin dukkan malamai sun hadu akan haramcin sayarda jini,
[AL-MUGNI & MUKHTARUL JALIYYAH-na SI'IDY]

5⃣➖CIRE WANI BANGAREN MAMACI DON SAWA RAYAYYE✔
   Duk gawa najasane amma banda na mutum,
💡ALLAH SW yace <<sai in yakasance mushene ko jininda aka zubar ko naman alade- shi najasane>> {SRT AN'AM-145}
▪IBN TAIMIYYA cikin SHARHUL UMDAH & IBN RIF'AH cikin HASHIYAR SHABRAMALSY sun anbaci ijma'i akan najasar mushe, dalilinda kuma yake nuna gawar mutum ba najasa bane=
💡ALLAH SW yace <<hakika mun karrama dan adam>> {SRT ISRA'I-70}
💡ANNABI SAW yace "musulmi baya najastuwa" (BHR & MLM)
💡Daga IBN ABBAS "kudaina najastarda mamatanku, musulmi baya najastuwa araye ko ya mutu"
   Don haka ya halatta yayin bukata acire wani gaba daga mamaci asawa rayayye don inganta lafiyarsa, amma da sharadin in mamacin ya bada izini kafin mutuwarsa ko magadansa sun amince sa'annan kuma yazanto kyautane ba da kudiba, domin bai halatta sayarda wani gaba ajikin mutum ba domin mallakar ALLAH ne ba nasaba,
[MUKHTARUL JALIYYAH & MAJMU'U FATAWA BN BAZ & UTHAIMEEN & QARARATUN WA TAUSIYYATU MAJMA'IL FIQHIL ISLAM]

6⃣➖AMFANI DA AMSA KUWWA📢🎤 A SALLA✔❌
   Idan na'urar ta kasance na daga muryace ko zakakashi ko kyautatashi- aiki dashi ya halatta,
   Idan kuma na'urace maimaita haruffa- aiki dashi ya haramta, domin zai sabautarda karin harafi ko haruffa cikin tilawar QUR'ANI sai yazanto ya canza maganar ALLAH,
[FATAWA UTHAIMEEN & SHARHU UMDATUL FIQH]

7⃣➖SANYA GAWA CIKIN FIRIJI✔
   Idan an sami jinkirin bizne gawa don gudanarda wasu bincike don zargin kisa ko makamancinsa- to ya dace asa gawa a friji don kada yakumbura ko yasauya ko rubewa, Sa'annan kuma duk lokacinda aka fito dashi daga frijin to ya halatta amasa wankar gawa koda yana daskare a kankararsa,
[FATAWA BN BAZ & SHARHUL MUMTI'I & FATAWAL LUJNATUD DA'IMAH]

👏🏻YA RABBANA KABAMU RAYUWA MAI KYAU A DUNIYA DA LAHIRA KUMA KATSAREMU DAGA AZABAR WUTAAAAA,
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via👉 Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽