KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐04/AL-MUHARRAM/1440-HJRY
🌐14/SEPTEMBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu

♦TOPIC👉 (SHEKARA TA BACE—WATA SHEKARAR TA BULLO)

NA KASASHI GIDA 6⃣

1⃣👉 SHIMFIDA‼
   Yaku bayin ALLAH a makonnanne shekarar 1439-HJRY yakare ranar litinin- nan take sabuwar shekarar 1440-HJRY takama ranar talata- yau juma'a har takai kwanaki 4,

2⃣👉 TSOKACI‼
   Kwanaki na tafiya❗shekaru na shudewa❗suna barin wa'azi, jarin mutum rayuwarsa, inya sarrafata a bautan ALLAH ya rabauta, in kuma a sabon ALLAH ya tabe,

3⃣👉 ABIN LURA‼
   Bayin ALLAH! mulura nawa muka bizne da hannunmu a wannan shekararda yakaren⁉daga malamai & senetoci & 'yan majalisu & sarakuna & talakawa & iyaye &' ya'ya & matasa & dattabai & Jami'an tsaro & 'yan ta'adda- wadanda suka mutu ta kisa ko hatsari ko hawan jini ko sukari ko taifod ko maleriya ko bugun zuciya ko ko ko......

4⃣👉 MUYI BA'ADY GA SHEKARARDA YA SHUDE‼
   Kowa cikinmu yayi tunanin me yagabatar a shekararda yawucen dama dukkan shekarunsa nabaya, ina yagaza? ina yayi kuskure? yayiwa kansa hisabi don sassauta na lahira, yatuba daga dukkan laifukansa don maye gurbinsu da lada,

5⃣➖MUYI QABLY GA SABON SHEKARAR 1440‼
   Yadda attajiri ke ajiye kayansa agaba karshen shekara don lissafi❗yadda matafiyi in yazo yasami hanyoyi sun rarrabu yake tsayuwa don nazarin wacce zata kaishi gaci- tofa muma ya wajaba mu tsaya muyi tunani da niyyar ninninka ayyuka nagari da barin akasinta da tuba akan zunabban baya dominfa an nadeta an kaiwa ALLAH,
 💡ANNABI SAW yafada a khuduba= Yaku mutane! lallene kunada mahalicci kufarka zuwa gareshi, kunada makarashi kufarfa zuwa gareta, mumini yana rayuwa tsakanin tsoro guda 2, lokutanda suka gabata baisan meye ALLAH yarubuta masa acikinsuba, hakanan lokutanda suka rage masa baisan meye ALLAH zai hukunta akansaba, kowa yaribaci rayuwarsa b4 mutuwarsa, samartansa b4 tsufarsa, duniyarsa b4 lahirarsa,
 ◾ABUBAKAR R/A yace= Yaku mutane kuna sammakawa da yammaci zuwaga ajalinda iliminsa ya buya agareku, in kun sami daman aiki mai kyau kuyi❗

6⃣👉 🌙 MUHARRAM & FALALARTA‼
 💡ANNABI SAW yace "watan ALLAH MUHARRAM (MSLM-1163)
 ▪SHEIKH ALMUNAJJID yace= jinginshi ga ALLAH jinginawane na girmamawa da daraja da falala, kamar yadda ALLAH yake jingina wasu kebantattun halittunsa da bayin sure gareshi, irinsu ANNABI MUHAMMAD SAW & IBRAHIM & IS'HAQ & YAQUB da sauransu, hakama yajingina KA'ABA🕋 & Taguwar ANNABI SALIH zuwa gareshi,
 ▪HASANUL BASARY yace= fiyayyen wata cikin watanni 4 masu alfarma shine MUHARRAM domin da ita ALLAH yabude shekara kuma yamaida ita cikamakin watanni masu alfarma, babu mafi girma wata bayan RAMADAN sai MUHARRAM,
 💡ALLAH SW ya haramtarda zaluntar kai a MUHARRAM da sauran watanni masu alfarma (SRT TAUBAH-36)
 ▪QATADAH tace= zalunci a watanni masu alfarma yafi girman laifi samada in a wani wata dabanne, dukda zalunci haramunne akoda yaushe, saidai ALLAH yana girmama abinda yaso cikin lamurransa,
(IBN JARIR & IBN KATHEER)

7⃣👉MUSTAHABBANCIN AZUMI A 🌙 MUHARRAM ‼
 💡ANNABI SAW yace "fiyayyen azumi bayan ramadan watan ALLAH Almuharram" yana nuna sakakken azumin nafila,
 💡ANNABI SAW yace "ashura yana daga yinnan ALLAH" (MSLM)
 💡ALLAH SW yacewa MUSA A/S <<katunatardasu yinnan ALLAH>> akwai ASHURA aciki,
 ▪SHEIKH ALMUNAJJID yace= ALLAH ya tseratarda MUSA A/S da mutanensa kuma ya hallakarda Fir'auna da dakarunsa ranar 10/MUHARRAM- ASHURA, ANNABI MUSA A/S yarika azumtar yinin don godiya ga ALLAH akan wannan ni'imar, hakama ANNABI MUHAMMAD SAW ya azumta kuma ya umurci al'ummarsa su azumta a mustahabbi, hakan yanuna tabbatarda alakar 'yan'uwantakar imani koda zamanin muminan bayan ya wuce kuma koda akwai tazara tsakanin garurrukan,
 ▪SHEIKH yacigaba dacewa= muguji bidi'oinda wasu ke aikatawa ayau na rikan wadannan kwanakin na bakin ciki da alhini da ihu don kashe HUSSAIN R/A ai musulunci tayi umurni da hakuri da haramtarda ihun mutuwa, hakanan muguji rikansu ranakun bukukuwa da girke girke da ciye ciye na  musamman don murnar kisar, kaci abinda kasaba ci,

❗NB= ni Abubakar BN Mustafa Biu ko kai ko ke dukda anfara shekarar damu- ba tabbas bane mukai karshenta‼
❗abin kukakane😭 shudewar shekara ba abin murnaba😄, donfa muna kara kusantar KABARINE‼

👏🏻YA RABBANA KASASHI MUCIKA DA IMANIIIIIIIIIIIIIIIIIIII,
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via= Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽