KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐27/ZUL-HIJJA/1439-HJRY
🌐07/SEPTEMBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA= Abubakar BN MUSTAFA Biu

⭕TOPIC= (KUNEMI TAIMAKO DA DARURUWANKU)

♦NA KASASHI GIDA 4⃣

1⃣➖MA'ANAR AYATA 6 A SRT MUZZAMMIL‼
 💡ALLAH SW yace <<lallene tashin dare itace mafi tsananin nutsuwa kuma mafi tsayuwar magana>> [SRT MUZZAMMIL-6]
 ◾IMAM QURTDUBY yace= ALLAH SW ya bayyana a wannan ayar falalar sallar dare akan sallar rana, kuma yawaita sallar dare da tsawaita karatunta yafi jawo girman lada,
  ▪IBN ABBAS R/A & MUJAHID & MALIK & IBNUL ARABY sunce=ma'anar (NASHI'ATUL LAILI- darene gaba daya domin yana tasowane bayan yini,
  ▪AISHA & IBN ABBAS R/A & MUJAHID sukace= NASHI'ATUL LAILI- shine tsayuwar dare bayan an taba barci, wanda yayi afarkon dare baiyi NASHI'ATUL LAILI ba,
  ▪YAMAN & IBN KAISAN sukace= shine tsayuwa karshen dare,
  ▪cikin ASSIHAH= NASHI'ATUL LAILI shine awonnin farkon dare,
  ▪AL-QUTBY yace= shine lokutan dare gaba daya,
➖Amma ma'anar fadinsa <<tsananin nutsuwa da tsayuwar magana>>
  ▪IBN ZAID yace= ma'anar said shine- yafi tsananin sanya muwafaka tsananin zuciya da gani da ji da harshe ❤👁👂🏽👅,
  ▪KUMA ANCE= tafi bada daman sarrafa tunani da lura,
  ▪QATADA & MUJAHID sunce= yafi datarda karatu da tabbatar dashi domin shi lokacine na fahimta,
((TAFSIRUL QURTDUBY))

2⃣➖SIRRIN NASARA DA TSIRA ACIKIN DARENE‼
 ◾DR KHALID IBN ABDULKARIM yana cewa= lallene dare musammanma ⅓ nakarshe yana daga mafificin lokutan zikiri, domin kwakwalwa alokacinnan yana cikin mafi kololuwar mafificin nutsuwa da wankuwar zuciya, kuma ga albarkar lokacin sakamakon saukowar ALLAH zuwa sama ta daya da kuma bude kofofin sama, kowacce abu a wannan lokacin kwakwalwa zata hardace kuma tatabbatu acikinsa,
   Don haka katashi kayi bitar karatuttukanka da tuna ideas a wannan lokacin,
   Dominfa dayawa cikin gwarazan duniya sunyi amfanine da wannan lokacin daga 'yan siyasa da 'yan tattalin arziki musammanma turawan yammacin duniya, domin mafi yawa daga cikinsu sunce suna bitar ilimukansu ko basirarsu ko takardunsu ko fikirarsu a wannan lokaci na ⅓ nakarshen dare,
   Don haka masu haddar QUR'ANI da nazarrukan addini su sukayi dacewa da moran wannan lokacin don dabbaka imaninsu da ilmukansu,
  ▪IBN ABBAS R/A yace= shine lokacinda yafi dacewa afahimci QUR'ANI,
  ▪IBN HAJR yace= JIBREEL A/S yana saukowa akowace daren RAMADAN suyi bitar QUR'ANI tareda ANNABI SAW, sirrin haka shine domin shine lokacin fahimta da nutsuwa, (FATHUL-BARY)
((MAFATIHU TADABBURIL QUR'AN- WANNAJAHI FIL HYATT))

3⃣➖MAGANGANUN SALAF AKAN KIYAMULLAILI‼
  ▪FUDAIL IBN IYAAD yace= idan rana tafadi ina farin ciki da duhun daren don samun kebantuwa da mahaliccina, idan kuma rana tabullo sai inyi bakin ciki....
  ▪IBNUL MUNKADIR yace= babu abinda yarage daga dadin duniya sai abubuwa 3, kiyamullai & haduwa da 'yan uwa & sallar jam'i,
  ▪MALIK IBN DINAR yace= idan bawa yatashi yana sallar dare ALLAH yana kusantowa daf dashi,
  ▪ALIYU IBN BAKKAR yace= yau shekaru 40 babu abinda yake bakanta mini rai kamar bullowar rana,

4⃣➖DAGA RIBAR RAYA DARE‼
   Ribar tanada yawa, daga ciki=
 ➖SAMUN ILIMI=
 💡ALLAH SW yace <<shin wanda kaskantarda a sa'o'in dare yana sujada kuma yana tsayuwar salla yana tsoron lahira kuma yana fatan rahamar ubanginsa, shin wadanda sukeda ilimi zasuyi daidaine da wadanda basuda ilimi? lalle masu hankaline kawai suke tunani>> [SRT ZUMAR-9]
 ➖SHIGA CIKIN JERIN BAYIN ALLAH ZABABBU=
 💡ALLAH SW yace <<bayin MAI RAHAMA sune wasanda.......... kuma wadanda suke kwana cikin dare tsakaninsu da ALLAH suna sujjada da tsayuwa>> [SRT FURQAN 63-64]
 ➖ALJANNA=
  💡ALLAH SW yace <<lalle masu taqawa suna cikin ALJANNA da idaniyar ruwa............ sun kasance lokaci kadanne suke barci da dare>> [SRT ZARIYAT 16-18]

👏🏻YA RABBANA KABAMU RAYUWA MAI KYAU A DUNIYA DA LAHIRA KUMA KATSAREMU DAGA AZABAR WUTAAAAA👏🏻
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

VIA= Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽