KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐11/MUHARRAM/1440-HJRY
🌐21/SEPTEMBER/2018-MLDY

🎙MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu

♦TOPIC👉
 [KAKIYAYE HARSHENKA] 👅
 [KAGUJI GULMA👅]

➖NA KASASHI GIDA 4⃣

1⃣➖HADARIN HARSHE👅‼
   Har zuwa yaushe zamu cigaba da gafala daga hadarin HARSHE⁉
 ▪IBN QAYYIM yace= "abin mamaki kaga mutum cikin sauki ya kiyaye kansa daga sata & zalunci & giya amma kiyaye HARSHENSA ya gagareshi,   lalle bawa zaizo ranar kiyama da kyawawan ayyuka kamar tsaunuka amma kash harshensa ya rusata, hakama zaizo da zunubbai kamar tsaunuka sai yatarar HARSHENSA ya rusata da yawan anbaton ALLAH" {ALJAWABUL KAAFY}
 ▪MUHD IBN WASI'U yace= kiyaye HARSHE ga mutane yafi wahala samada kiyaye kudi!

2⃣➖HADARIN HARSHE A QUR'ANI & HADISI‼
 💡ALLAH SW yace <<babu abinda mutum zai furta face akwai mai lura da kididdigewa>> {SRT Q-18}
 ◾IBN ABBAS yace= zasu rubuta duk abinda yafurta na alhairi da sharri harma da fadinsa- naci, nasha, natafi, idan aka kaisu a ranar alhamis sai aware na alhairi da sharri a watsarda sauran,
 💡ALLAH SW yace= <<lalle akanku akwai masu tsaro * masu girma masu rubutu>> {SRT INFDR-13}
 💡ALLAH SW yace= <<kada kayada abinda baka saniba, lalle ji da gani da zuciya abin tambayane akansu>> {SRT ISRA'I-36}

3⃣➖SALAFUS SALIH DA HARSHE👅‼
 👉 UMAR BN KHATDAB R/A yace tararda ABUBAKAR SIDDIQ R/A yanajan HARSHENSA yana cewa- wannan yajefani matsaloli! (MUWADDA)
ALLAHU AKBAR❗wannanfa fiyayyen bawa kenan bayan Annabawa da Manzanni,
 👉 Wani yaga IBN ABBAS rike da HARSHENSA yana cewa= kaitonki! kifadi alhairi kimore, kiyi shiru daga furta sharri ki kubuta,
Sai mutumin yacewa IBN ABBAS- meyasa naganka haka?
IBN ABBAS yace= shi bawa a kiyama babu abinda yafi tsana kamar HARSHENSA! (AHMD, IBN MBRK, ABU NA'IM)
 👉 ABDLH IBN ABI ZKRY baya bari a aibanta wani a majlisinsa, yana cewa= idan kun ambaci ALLAH zamu taimaka muku, in kuma kuna aibanta mutane zamu rabu daku!
 👉 TDAWUS IBN KAISAN yana bada hanzarinsa na yawan shiru yana cewa= na lura da HARSHENA natarar yanada matsala!
 👉 HASANUL BASARY yace= in munce- HAMIDU BAKI- muna tsoron kada yazanto gulma,
 👉 IBN SIREEN yana kwatance yace= wancan mutumin bakin,
Sai yace= ASTAGFIRULLAH, ina tsoron kada nayi gulmansa!
 👉 ABDLH IBN WAHAB yana cewa= na yiwa kaina bakance duk lokacinda nayi gulman wani sai nayi azumi yini guda, in nayi sai nayi azumi, da naga na kasa dainawa sai nayiwa kaina alkawari= innayi gulma zanyi sadaka da dirhami guda, don son kudina sai nabari,
 👉 BAKAR IBNUL MUNIR yace- naji IMAMUL BUKHARY yana cewa= inason in hadu da ALLAH kada yatuhumeni da nayi gulman wani,
 IMAMUZ ZAHABY cikin SIYAR yake cewa= IMAMUL BUKHARY yayi gaskiya domin duk wanda yake karanta maganganunsa cikin JARHI sai yaga yana tsantsini madadin yace wane makaryacine ko da'ifine sai yace= Hadisinsa munkar ne ko anyi shiru akansa ko akwai abin dubawa akansa, wannan matukane wajen wara'i,

4⃣➖RUFEWA DA AYOYI 2 MASU RUGUGIN TSAWA AKAN HARSHE👅‼
 💡ALLAH SW yace <<Yaku wadanda sukayi imani kada wasu mutane suyiwa wasu izgili maiyiwuwa sufisu, hakama mata kada suyiwa wasu mata izgili maiyiwuwa sufisu, kada kuyi zunden junanku kuma kada kujefi junanku da mummunanan lakubba, tir da sunan fasikanci bayan imani, wadanda basu tubaba to sune azzalumai * Yaku wadanda sukayi imani kuguji yawan zato lalle wasu zaton zunubine, kada kurika bincikan aibin junanku, kuma kada kuyi gulman sashinku, shin dayanku zaiso ya I naman da'uwansa mushe? to kuki masa, kuji tsoron ALLAH lalle ALLAH mai karban tubane mai jinkai>> {SRT HUJRAT-11-12>>

'YANUWA! cin mutuncin mutane bai takaita da harsheba harma zuwaga abubuwanda muke rubutawa na wayoyi da social media- bala'inefa, kadaina ruduwa da yawan comment don kaci zarafin malami ko wani bawan ALLAH!
YA RABBANA KASA MUWANYE LAFIYA,
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via= Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽